An dakatar da Muntari don 'kyamar' wariyar launin fata

Sulley Muntari Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Muntari ya ce bai ji dadin nuna wariya da aka yi masa ba

An dakatar da dan wasan Pescara, Sulley Muntari na tsawon wasa daya bayan da ya nuna rashin amincewarsa da wariyar launin fata.

An hukunta shi ne bayan da ya tunkari alkalin wasan a ranar Lahadi yana masa korafin cewa wasu magoya bayan Cagliari sun ci zarafinsa, matakin da ya jawo alkalin wasan ya nuna masa yellow kati.

Dan wasan dan asalin kasar Ghana mai shekara 32, ya fice daga filin wasan domin nuna rashin amincewarsa, matakin da ya sa aka ba shi yellow kati na biyu in ji jami'an wasa.

Kwamitin ladabtarwa na hukumar gudanar da wasan kwallon kafa na Italiya Serie A, ya amince cewa abin da magoya bayan suka yi bai dace ba, suna cewa ba zasu dauki matakin ladabtarwa ba tun da masu laifin ba su wuce 10 ba, wanda suna kasa da kashi daya cikin 100 na magoya bayan kulob din Cagliari da ke wurin.

Amma Garth Crooks, tsohon dan wasan kwallon kafa na kungiyar Tottenham ya kalubalanci "dukkan dan wasan kwallon kafa bakar fata mai kishin kansa" da ya kauracewa filayen wasannin karshen wannan makon a kasar Italiya, idan dai ba a dage hukuncin dakatar da Sulley Muntari ba.

Kungiyar Kick It Out mai yaki da nuna bambancin launin fata, ta yi Allah-wadai da matakin da shugabannin kungiyar kwallon kafa ta Italiya suka dauka, inda ta kira su "marasa zuciya", a sanarwar da kungiyar ta fitar a shafinta na Twitter.

Ta kara cewa "Dole masu ikon fada a ji a Italiya su dauki matakin hana faruwar irin wannan lamarin nan gaba".

A wata sanarwar da kungiyar ta Kick It Out ta fitar a shafinta na yanar gizo, ta bayyana Garth Crooks yana "kira ga dukan bakaken fata dake buga wasan kwallon kafa a kasar Italiya da su kaurace ma filayen wasannin har sai an janye matakin ladabtarwar da aka yi ma Sulley Muntari".

A ranar Talata kungiyar 'yan wasan kwallo ta duniya, Fifpro ta yi kira da a janye hukuncin da ke kan Muntari - duk da cewa basu san an ba dan wasan yellow kati na biyu ba.

''Muntari na da ikon ya kusanci alkalin wasan," in ji kungiyar ta Fifpro.

Inda ta kara da cewa ''Kamata ya yi 'yan wasa su iya kusantar alkalai, musumman ma a kan batun zargin wariyar launin fata.

''Muna kira ga hukumonin Italiya da su ba Muntari damar bayyana abin da ya faru, kuma su gudanar da bincike a kan lamarin kana su dauki mataki domin tabbatar da hakan bai sake faruwa ba.''

Idan ba a manta ba, dan wasa Kevin-Prince Boateng ya taba ficewa daga filin wasa a watan Janairu na 2013, a lokacin wani wasan sada zumunta da kungiyar Pro Patria domin wasu 'yan kallo sun ci zarafinsa domin launin fatarsa.

Mista Boateng ya nuna goyon bayansa ga Muntari a kan shafinsa na Twitter yana cewa, ''ina alfahahi'' da tsohon abokin wasansa.

A halin yanzu kwamitin ladabtarwa na Italiya ya yi gargadin cewa zai kulle filin wasa na Lazio da Inter Milan, idan mogoya bayansu suka sake nuna wariyar launin fata.

Labarai masu alaka